Burinsa ya cika

   Salamu alaikum waraha matullahi ta'ala wabaraka tihu, 
Sunana Sadiku yusuf , acikin sharhin namu na yau zakuji abinda ke faruwa musamman dan gane da binne Alhaji Alhasan Dan Tata a birnin madina , Kano ta hada wata tawaga mai karfi don halattar binne marigayin a madina,
Wanda sun hada da sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu ,da gwamnan kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da manyan jiga jigan gwamnati, kuma harda Sarkin kano na sha biyar Alhaji Aminu Ado Bayero, shima anasa bangaren ya halicci ja na'izar, hukumar saudiyya ta amince da abinne marigayin wanda yai dai dai da wasiyyar da ya bari ,Allah ya cika masa burinsa na tabbata a kushewa madina.

 A wani labarin kuma anyiwa iyalan wanda suka rasa ransu 
a hadarin mota su kimanin ashirin da biyar ,wato yan wasan da suka wakilci jihar Kano a kakar wasanni ta bana a hanyarsu ta dawowa bayan an kammala wasan ,iyalansu sun samu ta gomashi daga gwammnatin tarayya da ta jiha da kuma dai dai kun mutane ciki har da yan majalisu masu ci.inda sanata Barau Jibrin Maliya yabada naira Milan ashirin da biyar ,haka itama Remu Tinubu ta bada million dari haka itama tawagar gwammnatin tarayya ta bada nata taimakon ga iyalan haka dai ake ta kawowa.
 Ita kuma gwammnatin Kano, tace baza'a manta da yan wasanba a dalin haka aka sanya sunan yan wasan a kwalejin wasanni  da kuma wasu mahimman gurare fomin arika tunawa dasu da fatan Allah ya jikansu da rahama in tamu tazo Allah yasa mu cika da imani amin.

 Sai shrhi kan al'amuran yau da kullum, yau zami dubane 
da Danjoji da gwammnatin kajo ta Alhaji Abba Kabir Yusuf  ta samar dasu don bin doka da kai'dar titi kusan ko' ina cikin brnin Kano da kewaye ansa su , to amma wani abin ta kaici sai kaga mutane basa bin dokar wannan danja , kowa inyazo baya san tsayawa motoci manya da kanana har da babura masu kafa uku wato Adai daita sahu, da kuma kananan babura abin ba dadin dadin gani kuma hakan zai zama musabbabin hada hadari yakamata mutane su san cewa su akaiwa wannan danja dasu lura subi foka don samun saukin chinkoso ,in mutum yayi hakuri baya wuce minti biyu azo kansa, sai mukula don samun cigaban birninmu baki daya, kuma in mutum ya lura zaiga cuwa an kawata birnin da wa yan nan danjoji da futulu. 

  A wani labarin yan sandan jihar zamfara sunkashe rikakken dan bindiga da ya addabi wasu sassan jihar zamfara,wayo dan Bokolo a cewar gwammnatin jihar ta bakin mai baiwa gwamna shawara kan harkokin tsaro wato Ahmad Manga inda yace kisan nasa yasa ansamu gagarumar nasara saboda sun addabi jihar dake arewa maso gabas ta Nigeria wannan rikakken dan bindiga shine uban gidan Bello Turji ,yafi Bello Turji fitina kawai dai Bello Turji yafishi sunane inji Ahamad Manga. Wannan mutum yajanyo mutuwar akallah mutum dari ata bakinnasa.

Dan Bokolo yarasa ransane awata arangama da akai a kauyen Kurya tsakaninsa da yan sa kai na gwamnatin jihar
Da kuma mayakan dan Bindiga, ana kallon kisan nasa a matsayin gagarumar nasara a wajen yaki da yan Bindigar
Dan Bokolo ya dade yana addabar yankin zamfara wajen kai hare hare da kuma satar mutane domin kudin fansa,basa tausayin alumma kuma suna kiran kansu wai su musulmine ko yace haka mulunci yake shi mutumne mara imani ko kadan bai yadda da sulhuba kamar yadda dan uwansa Bello Turji yataba nunawa abaya inji wani mazaunin yankin, Allah ya kawo karshen zub da jini a arewacin Nigeria da diniya bakidaya amin summa amin, mai rubutu shine .
  Sadik Yusuf Kano, 
 Za'a iya tun tubarmu a imel namu .
 Sadiku854@gmail.com. 

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

YAR MALAM SEASON 1 EPISODE 1 review

Nigeria a yau