Janai’zar Buhari
Dandali namu na musamman wato NishadiSport, inda muke kawo muku labarai da kuma sharhi kan al’amuran yau da kullum da kuma bayani kan wasu shirye-shiryen fina-finai.
Ni ne naku Sadik Yusuf, ga abinda zamu gabatar.
Bayanan Jana’iza
Bayan shafe lokaci ana dakon gawar tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari, a ƙarshe dai an kawo gawar tasa daga kasar ingila inda yake jinya. Anyi salar gawa a gudansa fake Daura An binne gawarsa a ranar Talata, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu. A filin gidansa fake Daura.
Jana’izar ta samu halartar dubban mutane daga ciki da wajen Najeriya. Ciki har da:
- Shugaban ƙasar Chadi
- Shugaban ƙasar Guinea
- Firayim Ministan ƙasar Nijar
- Shugaba Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibril
- 'Yan majalisa, tsofaffi da masu ci
- Gwamnoni, sarakuna daga kudu da arewa
- Malamai da talakawa
A wajen sallar jana’iza a filin saukar jirgi na gidan nasa, an ga Gwamnan Katsina, Umar Dikko Radda, yana zubar da hawaye. An binne Buhari a cikin gidansa. Ya rasu yana da shekaru 82. Ya shugabanci Najeriya ta soja tsawon wata 20, sannan ta farar hula na tsawon shekara 8.
Rayuwarsa
Ya yi gwagwarmaya a rayuwarsa. Ya jagoranci korar sojojin Chadi. Ya rike mukamin PTF (Petroleum Trust Fund) ƙarƙashin General Sani Abacha, inda ayyukansa suka bazu ko’ina a ƙasa.
Har mutane suka kara sanin halayensa na taimako, da kuma matasa wanda basuyi zamani dashiba sima hakan yasa sun kara saninsa shi isa farinjinisa ya ninku fiye da duk wani dan siyasa a kasar.
Inda talakawan kasar suka rika tara kudi da niyyar sayen fom na tsayawa takara wanda a tarihin Nigeria ba'a taba samun wanda aka yiwa hakaba sai shi Muhammadu Buhari,haka lamarin yake Allah mai yadda yaso.
Ya shiga harkokin siyasa inda ya fara kalubalantar chef olusegun Obasajo, inda ya tsaya takara har sau uku baya yin nasara,sai daga bisani ne yasamu nasara wanda har ya midday rai da sake tsayawa zabe inda yace:
"jiki magayi" yan Nigeria kudu da arewa sun bashi amanna cewa za'a damu saukin al'amura a kasar musamman aiyukan yan ta adda, da tashin farashin ka yayyaki.
Tsokaci
Wannan shi ne ƙarshen duk wani mutum, ko waye shi – ko da mai kudi ne, mulki, sarauta, soja ko talaka.
Komai kake takama dashi karshen alawa kasa. Sanda Buhari yana raye yafadi wannan kalma.
Karshen mutum – wannan ɗan karamin ramin za a sa shi. Iyalanka, masoyanka, har da makiya ba zasu hana hakan ba. Ana gani, ana ji, sai a tafi da mutum – daga kai sai halinka.
Wannan halin naka shi zai taya ka zama a barzahu, domin akwai rayuwa bayan mutuwa. Ka tuna iyayenka sun mutu, 'yan uwa da shugabanni – ba wanda ya dawo bayan mutuwa.
Amma mutane da yawa basa wa'azantuwa:
- Manya da kanana suna aikata barna
- Maciya amana
- 'Yan damfara
- Hanci, zamba, sata
- Kin biyan bashi
Allah baya yafe hakkin wani idan ba a biya shi ba.
Sai anyi disability mutum ya biya abinda yaci na wani ko mutum yasani ki bai saniba Allah ya sa muui kyakyawan karshe amin.
Tambayoyin Kabari
A kabari, za a yi maka tambayoyi.
- In ka bada amsa daidai, za a nuna maka gidanka a Aljanna. Ace ka kwanta cikin aminci.
- In ka kasa, za a nuna gidanka a wuta. Ka samu rasiin aminci ga macizai da kunamu Allah ya kisahemu amin.
Muna neman tsari daga wuta. Muna neman aljannarka, Ya Allah. Kaine mabuwayi mai kowa mai komai
Kiyaye Zuciya da Hakkokin Mutane
Muji tsoron Allah, mu kiyaye zalunci. Mu kare hakkokin mutane.
“In ka cinye hakkin wani – gida, fili ko kudi – ka tuna kai ma zaka mutu. Koda ace wanda ka zalunta ya mutu, kai ne za ka biya. Magadanka ba zasu biya ba – kai ne Allah zai tambaya.”
Yanayin Gawa
Wannan shine kwatankwacin yadda mutum ke zama a kabari:
- Jiki ya fara rubewa
- Tsutsotsi su fito
- Warin gawa ya bazu
- Naman jiki ya narke
- Ƙashi ya rarrabewa
Haka mutum zai kwanta har ranar tashin kiyama.
Muji tsoran Allah mudena daukar kayan mutane cin amana,zalunci,giba,da shan giya,zina da cha-cha wannan duk muna nan abu buwane.
Haka uwa uba kisan kai,wanda yazama ruwan dare a al'ummar mu ta hausawa da duniya baki daya. Kuma Allah yayi hani da kisan kai, mazonsa yayi tsoratarwa game da haka.
Wanda yakashe rai a kasheshi, in kuma ba'a yankewa mutum hukunciba to zai gamu da fushin Allah, zai dawwama a wuta har abada.
inkuma da kuskurene to zai biya diyya,kuma zai yi azumi guda sittin, wanda haka a kuskure kenan,don haka muji tsoron Allah mudena zubda jini ko masu sauki a wannan yanayi da muka samu kanmu a ciki a kiyaye.
Kammalawa
Allah ya datar damu.
Ya bamu ikon amsa tambayoyin kabari.
Muna neman Aljanna. Muna tsoron Azabar Allah daga wuta.
Ni ne naku, Sadik Yusuf,
Za ku iya tuntubata ta: 📧 sadiku854@gmail.com
Na gode!
Comments
Post a Comment