Assalamu Alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu
Masoya da mabiyan shafinmu mai farin jini wato NishadiSport, barkanmu da sake saduwa a cikin sabon cigaba na shirin Yar Malam.
A yau, zamu kalli abubuwan da suka faru a tsakanin Ladidi, Mama, da kuma Dogo da abokan sa. Ku biyo mu.
Mama Ta Kamu da Zazzabi – Ta Yi Nasiha Kafin Ta Rasu
Mama tana fama da rashin lafiya sosai. Jikinta yayi zafi, tana kyarma, sai ta kama yi wa Ladidi nasiha da kuka, tana cewa:
“Ladidi ki ji tsoron Allah, ki rike addininki, ki guji bin shaidan da rudin zamani kuma ki kula da addininki, ki rike bawan Allahan nan fa yatemakeki.” ita fai Ladidi tana kallon ikon Allah nan da nan sai hawaye ya cika mata ido.
Ladidi ta katse ta, tace:
“Mama ki daina irin wannan maganar. Domin kina fitgitani. Haka Baba ma yana yimin irin wannan nasiha sai kawai na ga ya mutu. Don Allah Mama ki daina!”
Mama ta kalli Ladidi, ta ce:
“Ba komai. Bawani abu bane kawai dai nasihace nake miki, kinsan akowane lokaci iyaye suna iya yiwa 'ya'yansu nasiha kar ki damu Allah yana tare da mu.” ita dai Ladidi kuka take tana taba jikin Maman nata tana dada lilli beta.
Ladidi:
Sai tace "bari naje na nemo mana taimako musamu mu sai magani" sai ta tashi ta tafi.
Ladidi ta tafi neman taimako domin basu da kudin magani balle na abinci. Amma tana dawowa sai ta tarar da Mama ta mutu.
Ladidi tayi sallama taji shiru ta karaso ji,i a sanyaye tasa hannu ta taba maman tata taga fai bata motsi, a'a ta girgizata taga dai ba alamr motsi Tai mata magana amma bata amsa ba. Nan Ladidi ta fashe da kuka.
Tana cikin kuka, sai kawarta ta shigo cikin gidan ta ce:
“Ladidi, me ke faruwa?” Ladai tana ta kuka "wai bazaki maganaba ne"
Ladidi ta ce:
“Mama ta mutu wayyo Allah na duba kigani.” kawa tasa hannu ta duba, ta Bude fuskar Mama taga ba alamar motsi, nan da nan ta tashi da sauri.
Kawar ta ce:
“suba hanallah inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.Bari na tafi na kira Malam Idi! Kiyi hakuri ki daina kika kiyi ta yimata addu'a kafin,mudawo” ta garzaya da gudu takira Malam Idi.
Sukazo da makota aka taru akayima Mama suttura aka binne ta
amma Malam idi ya hana kowa zama domin karbar addu'a sai kawai Ladidi kafai aka barj a gidan saboda tsabar rashin mutunci.
Dogo da Magatakarda Sun Yi Murna da Mutuwar Mama
A daya bangaren kuwa, Dogo da abokinsa Magatakarda suna murna da mutuwar Mama. Suna ta tintsira dariya suna cin gyada wai Mama ta mutu ana shagali.
Sai kace su bazasu mutuba, akiyayi duniya kowa yana tafe indai mutuwace.
“Yanzu ne zamu sakata mu wala mu shiga gidansu su Ladidi domin wawure komai,” inji Magatakarda.dogo yana cin gyada yana ta dariya abinsa.
Dogo:
"Ai mun yar da kwallon Mangwaro mun huta da kuda yanzune zamu sakata muwala, umar ladi ta muru (kawu kalata),yanzu sai yadda mukayi da Ladidi, daman uwartace take taka mana birki wani lokacin."
Magatakarda ya ce ya sanar da Gurgu ya turo ’yan daba daga birni domin su rika kare su daga duk wanda zai zo cikin harkar. Dogo ya yarda cewa hakan yayi kyau, domin wanda yake cikin rayuwar Ladidi yana da Ζarfi, dole a dauki mataki a kansa.
hakane inji Dogo "domin wannan wanda yashigo rayuwar Ladidi Yana da karfi don haka dole ne musamu yanda zamu tinkareshi." Suka tafa.
Sani Ya Kori ‘Yan Daba – Gurgu Ya Fusata
Yaran Gurgu sun iso, amma sun hadu da Sani – wanda ya rufe musu hanya. Duk da yawansu, Sani ya basu kashi yai musu fafata mai tsanani. Sun sha kashi a hannunsa. Suka koma wurin Gurgu da kukan rashin nasara.
Gurgu ya fusata, yace:
“Yanzu haka zakuyimin kuce yafi karfinku ro yanzu me zance da dogo, inko kun kasa komai zaku koma birni. Wallahi kun bani kunya!”
Sai suka ce masa:
“Oga ba matsala. Daga yanzu zamu san yanda zamuyi dashi. Sai mun kamo shi, ko ta halin kaka zamu yi nasara a kansa.”
Yaran Gurgu Sun Juya Masa Baya
Duk da cewa Gurgu ne ya kawo su daga birni, sun juya masa baya suka koma bin Dogo da Malam Idi. Dalilinsu kuwa shine suna samun kudi da abinci da lemo daga Dogo, kuma Magatakarda na basu duk abin da suke bukata.
Wata rana sai aka turo su da wani aiki kamar yadda aka saba – a kain su kaiwa soja hari wanda shine Baban Gurgu. Gurgun da ya kawosu.
Soja Ya Gano Cewa Dansa na Cikin Makirci
Soja ya sanar da Gurgu cewa wasu mutane na shirin yi masa mummunar illah. Kuma malam Idi ne yake turosu domin su raunatani Sai Gurgu yace:
"ai basu da mutunci bari na turo wasu yara su baka kariya zanyi maganinsu."
“Kai Muzali! Ka hadani da su domin su bani kariya fomin naga suna da hadari."
Gurgu ya ce:
“Kai Baba, kayi hakuri. Zan gaya maka a gida.”
Yaran suka ce:
“Ai Baba Idi ne ya ce mu dakaka. Ba za mu saba da umarninsa ba.”
Gurgu ya ce:
“To kuyi hakuri, don ni ubanane.”
Suka ce:
“Ai ma sai mu hada da kai ma dukan! Domin mu masu biyayya ne ga Baba Idi da Dogo da Magatakarda.”
Inna Ce Kadai Ta Rage da Hankali
A gefe guda kuma, Inna (maman sace) kadai ba ta goyon bayan sharrin da Malam Idi da Dogo suke aikatawa. Tana kokarin ganin an daidaita lamura.
Amma sun takuramata – ba su barinta tayi abin da ta ga dama balle ta huta.
Ku Ci Gaba da Bibiyar Shirin "Yar Malam"
Kada ku manta, ku biyo shirinmu na musamman "Yar Malam" a tashar mu ta YouTube: NishadiSport, don ganin yadda wannan rikici zai kaya – shin Ladidi zata kubuta? Shin Dogo da Magatakarda zasu ci nasara?
Tuntube Mu
✍️ Mawallafi: Sadik Yusuf
π§ Imel: sadiku854@gmail.com
π± WhatsApp: 08148166212
Mungode da kasancewa da mu! Kada ku manta ku yi subscribe a tashar NishadiSport.
Ku raba wannan shirin domin ya isa ga wasu.
Ku nemi wannan film kusha kallo
ReplyDelete