Mahaukaci da gata
Ashe maigari Yana da wani da da yake dukan mutane, rannna ana zaune a fada ana karbar gaisuwa Sai gashinan da katon Sanda ya nufo fada aiko yan fada naganin haka sai suka tashi zasu ruga Sai mai gari yace kutasaya ai baya komai in anfada masa wata magana, sarkin fada yace a to me ake fada Masa saboda bacin Rana, mai gari yace to bari kugani Ga abinda ake fadamasa da zar kaga yataho zai dokeka, Sai kace in anbi rabbana, to ba abin da zaiyi aiko Nandan suka ce in anbi rabbana Sai mahaukaci yace ba wahala nawa Sai ya nemi guri ya zauna.
Daman haka lamarin yake, ka zama mugu kaima kahadu da abinda ba yanda zakai dashi Sai kallo, Liman Yana bada labarin Dukan da mahaukaci yayimasa shine mahaukaci yaduro gun suka rikice.
Hoton mahaukaci
Rannan wata yarinya ta jefar da wani abu aiko Sai a fuskar shi wannan mahaukaci yana taso mata Sai tace 'in anbi rabbana'sai yace bawahala tawa ai ko daga ranar nan ya dafe mata Wai shi sonta yake tana Jin tsoronsa tasamu dai ta sulale suka rabu dash, Shi kenan duk inda yaganta sai ya bita Yana gaisheta. Itako Kawa kullum tsoransa take amma haka dai take hakuri da shi a tsorace tana Kuma yin addu'a haka take samun nasara a kansa shi Kuma yana ta fadi tashin nemanta kullum in bai gantaba ya Kama bugun mutane haka dai ake ta fafatawa kullum tsakanin Ladidi da Malam Idi da Kuma su Dogo,mahaukaci da alumnar gari da Kuma Kawa ga Kuma maigari da Malam Idi.
Watarana kawa taje gun Ladidi Dan neman shawara kan batun mahaukaci, Ladidi ta jin jina wannan lamaria wai mahaukacine yake son mace mai hamkali,Ladidi tace to abinda za'ai ni aganina kawai ki kama Allah ki rike shi hannu biyu gami da yin addu'a zaki Sami ma fita domin kuwa kinga nima addu'a ita na rike nake samun sauki gun
Mugayen mutanennan Dogo da Magatakarda gami da Babansu, yanzu har Allah ya kawo min sauki ta hannun wani wanda bai san komaiba a rayuta, don yafisu karfi da temakon Allah subhanahu wata ala tsarki ya tabbata a gareshi ,nasamu sauki don haka kema ki rike Allah shi zai miki maganin wannan mugun mahaukacin . Rife bakinta ke da wuya,sai ga mahaukaci kamar an jefoshi sai kawa ta kama addu'a kamar yadda aka bata shawara, aiko sai ya durkusa yana bata hakuri yana gaisheta su kuma suka kalli juna suna mamaki, suka samu suka sulale shi kuma yanacewa da da kawa, I LOVE tawa su kuma suna gudu a haka ya kyalesu ya tafi abinsa yana dariya,
Shikuma sani yata faman neman Ladidi suka yi kicibis da mahaukaci ,mahaukaci yana ganin Sani ya ranta ana kare ya ruga da gudu yai cikin gari ,shiko Sani yabishi da dariya ya tafi abinsa yacigaba da neman Ladidi yana ta fadi tashi a cikin unguwa amma ya rasa sai yakoma gida
ya shaidawa ma haifinsa yakasa samun Ladidi, ma haifin yace kar yadamu ya cigaba da nema wataran za'a dace bai kamata ace anwofantar da itaba, hakane baba inji Sani yayiwa ma haifin nasa godiya yatashi ya tafi.
Ma haifin Sani kenan
Wannan Shiri namu wato Yar Malam yana nan yana gudana a YouTube channel dinmu wato nishadisport a manhajar youtube mungode naku har kullum sadik yusuf
Wanda ya wallafa Sadikyusuf za'a iya tun tubarmu ta imel , sadiku854@gmail.com
http//: nishadisport.blogspot.com
Abin yayi
ReplyDelete